Rikicin siyasar Ireland

Brian Cowen
Image caption Brian Cowen zai ci gaba kan mukamin Fira Minista

Fira ministan Ireland Brian Cowen ya ce, zai ci gaba da kasancewa akan mukaminsa har zuwa lokacin babban zaben kasar da za a yi a watan Maris, duk da murabus din da ya yi daga kan mukaminsa na shugaban jam'iyya mai mulki ta Fianna Fail.

Ya ce duk da yake ya sauka daga shugabancin jam'iyyarsa, ba zai sauka daga kan mukamin Fira Minista ba.

Sai dai jam'iyyun hamayya sun ce, yin hakan ya sabawa tsarin dimokradiyya, kuma sun yi kiran a matso da babban zaben kasar kusa.

Rahotanni sun ce rudanin tattalin arzikin da Ireland ta fada ne ya haifar da rikicin siyasa a kasar.