ECOWAS na neman izinin kai hari Ivory Coast

Ministan harkokin wajen Najeriya Odein Ajumagobia, ya yi kira ga kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya da ya bada izinin amfani da karfin soja a kasar Ivory coast, don kara matsin lamba ga Laurent Gbagbo ya mika mulki.

Ajumogobia wanda ya yi wannan kiran a wani sharhi da ya rubuta a jaridar Thisday ta da ake wallafawa a Najeriya ya ce rikicin wanda laurent Gbagbo ya haddasa shi kadai ka iya rikidewa ya zama yakin basasa matukar ba a warware shi ba.

Ministan harkokin wajen na Najeriya wanda har wa yau shi ne shugaban majalisar ministocin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma ECOWAS, ya rubuta cewa kungiyar tana bukatar goyon bayan kasashen duniya kai tsaye ba tare da wani nuku-nuku ba, ta hanayar kudurin kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya da zai bayar da damar daukar matakin soji a kasar ta Ivory Coast.

A sharhin wanda ministan ya rubuta a shafin karshe na jaridar Thisday, ya ce yin hakan, ne kadai hanyar da za ta halasta daukar matakin soji daga kasashen waje domin magance zaman dar-dar da tashe-tashen hankulan da ake fama da su a kasar ivory Coast da ma yankin yammacin Afrika baki daya.

Matakin soji za ta kasance haramtacce

Ministan harkokin wajen Najeriyar ya kuma ce duk wani matakin soji da kungiyar ECOWAS za ta dauka kan kasar ta Ivory coast zai kasance haramtacce, matukar Majalisar Dinkin Duniya ba ta buga hatiminta na amincewa da daukar matakin ba.

Ajumogobia ya kuma kara da cewa, amfani da karfin soji, ba dole ne a ce yana nufin afkawa kasar da yaki ba , a 'a, hakan na iya nufin toshe hanyoyin shiga kasar ta ruwa don zartar da takunkumin da aka sanya wa Laurent Gbagbo.

Wasu na ganin cewa, kungiyar ta ECOWAS, ta sake nazari ne a kan kurarin da ta yi na daukara matakin soji a kan kasar ta Ivory Coast, saboda wasu dalilai.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonatahan dai shi ne shugaban kungiyar ECOWAS wadda ta yi barazanar daukan matakin soji a kan kasar ta Ivory Coast muddin laurent Gabgbo bai sauka ba ya mika mulki ga Alassane Ouattara, mutumin da kasashen duniya suka amince shi ya lashe zaben shugabancin kasar.

Wasu masu sharhi a kan al'amura na ganin cewa kasashe irinsu Najeriya za su yi taka tsan-tsan wajen tura dakarunsu zuwa wata kasa a wannan yanayi da suke tunkarar zabe a wannan shekrar, yayinda a wasu kasashen za a yi musu kallon ba su da bakin magana, ganin cewa ana zargin su ma shugabannin da suke mulki ba su ci zabe ba.