Hezbollah na yunkurin kafa gwamnati a Lebanon

Saad Hariri
Image caption Saad Hariri

Magoya bayan Praministan rikon kwarya na Lebanon, Saad Hariri, sun zargi kungiyar masu fafutuka ta Hezbollah da laifin neman kifar da gwamnatin kasar.

Kafofin yada labarai na kasar ta Lebanon sun ce daruruwan jama'a sun fito kan titunan biranen arewacin kasar, don nuna adawa da yunkurin kungiyar ta Hezbollah na kafa sabuwar gwamnati.

Tun farko dai kungiyar ta Hezbollah da kawayenta sun samu cigaba a yunkurinsu na nada wani attajiri da ya yi karatu a Amirka, Najib Mikati, a matsayin sabon Praminista.

Gwamnatin Mr Hariri dai ta wargaje ne, saboda goyon bayan da ta nuna ga wani binciken Majalisar Dinkin Duniya dangane da kisan mahaifinsa, Rafiq, a shekara ta 2005.

Binciken ya gano cewa akwai hannun kungiyar Hezbollah a kisan.