Mutane 35 sun hallaka a harin filin jirgin Moscow

Hari a filin jirgin saman Moscow
Image caption Hari a filin jirgin saman Moscow

Mutane 35 sun hallaka, wasu karin da dama kuma suka samu raunuka, a wani harin bam da aka kai a filin jirgin sama mafi zirga-zirga a birnin Moscow.

Masu bincike na Rasha sun ce wani dan kunar bakin wake ne ya tada bam din a harabar filin jirgin sama na Domodedovo.

Wasu hotuna da aka dauka a wayar salula sun nuna hayaki na tashi daga ginin da kuma gawarwaki a warwatse a kasa, sannan kuma jama'a dake wurin a firgice.

Shugaba Dmitry Medvedev ya ce zaa yi farautar wadanda suka kai harin domin hukunta su.

Wannan dai shine hari mafi muni da aka kai a birnin na Moscow tun cikin watan Maris din da ya gabata, lokacin da wasu 'yan kunar bakin wake 2 suka hallaka mutane 40 a tashar jirgin karkashin kasa ta birnin.

Kasashen duniya sun yi Allah wadai sosai da wannan hari.