Ouattara ya nemi a daina fitar da koko daga Ivory Coast

Alassane Ouattara

Mutumin da kasashen duniya suka dauka a matsayin shugaban kasar Ivory Coast, Alassane Ouattara ya nemi a dakatar da fitar da koko daga kasar zuwa kasashen waje.

Ya ce ya kamata a daina fitar da kokon na tsawon wata guda domin kara matsin lamba akan abokin adawarsa, Laurent Gbagbo, wanda ya ki mika masa mulkin kasar.

Shi dai Alassane Ouattara wanda ke zaune a wani otel da ke birnin Abidjan, ya rubuta wasika ga masu fitar da koko daga kasar ta Ivory Coast inda ya umarcesu da dakatar da fitar da kokon daga yau Litinin.

Wannan mataki dai na da nufin toshewa Laurent Gbagbo hanyar samun kudaden da zai ci gaba da kasancewa akan mulki.