An tona asirin dangantakar Palasdinawa da Isra'ila

Mahmud Abbas
Image caption Shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas yana ganawa da wakilin Amurka George Michele

Wasu takardun sirri da aka wallafa kan tattaunawar samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya sun nuna cewa, bangaren Palasdinawa ya taba amincewa da mamayar da Isra'ila ta yiwa yankunan gabashin birnin Kudus.

Gidan talabijin din Aljazeera da kuma jaridar Guardian da ke London ne dai suka wallafa takardun.

Takardun sun nuna cewa, gwamnatin Palasdinawa ta baiwa Isra'ila wannan gagarumar dama ne a shekara ta 2008.

Har wa yau bayanan sun nuna yadda Isra'ila ta sanar da wasu shugabannin gwamnatin Palasdinu aniyarta ta kaddamar da yaki a yankin Gaza a shekara ta 2008 da kuma shekara ta 2009.

Bayanai da na nuna cewa, nan da kwanakin dake tafe za'a fitar da karin wasu takardun sirrin da dama da suka shafi irin yadda gwamnatin Paladinawa take musayar bayanan sirri na tsaro tsakaninta da gwamnatin Isra'ila.

Mayar da martani

Manya-Manyan bangarorin da ke wakiltar al'ummar Palasdinawa sun maida martani a fusace a kan bayanan da aka kwarmata.

Kungiyar Hamas, wadda ke iko da zirin Gaza, ta ce takardun sun nuna yadda hukumar Palasdinawa ta amince da mamayen Israila.

Image caption An dade ana nuna shakku kan jagoran Palasdinawa Mahmud Abbas

To amma Shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas, ya ce akwai kuskure akan yadda aka gabatar da matsayin Palasdinawa a takardun.

Shi ma Babban mai shiga tsakani a bangaren Palasdinawa, Saeb Erekat ya bayyana shakku akan sahihancin takardun sirrin da aka kwarmata.

Yiwuwar zanga-zanga

Ana saran gudanar da zanga zanga nan da wani dan lokaci a can wajen ofisoshin Aljazira da ke tsakiyar Ramalah.

Mambobin jam'iyyar fatah ta Shugaba Abbas na bakinciki sosai game da takardun da aka kwarmata.

BBC dai har ya zuwa yanzu ba ta kai ga tabbatar da sahihancin bayanan ba. Ga alamu dai 'yan kasar Palasdinu sun sha mamaki sosai.

Batun shi ne bawai kawai shugabanninsu a shirye suke su mika wuya game da wasu manyan batutuwa ba a, abin bakin cikin a wajensu shi ne Isra'ilan tama ki amincewa da abinda suke so kai tsaye ba tare da wata kunbiya-kunbiya ba, abin da ke nuna raunin matsayin Palasdinawa.

Kungiyar Hamas

Sami Abu Zuhri mai magana ne da yawun kungiyar Hamas, ya ce bayanan da aka kwarmata game da Hukumar Ramallah takardu ne masu hatsari.

Kuma takarddun na yin nuni da cewar hukumomin Palasdinu suna bada kai ga mamayar Isra'ila.

Za 'a kwarmata wasu karin daruruwan takardun bayanan nan da wasu 'yan kawanki.

Takardun bayanan za su bada cikakken bayani game da irin abubuwan da Palasdinawan suka ce za su yi sassuaci akai.