Harin Bam a filin saukar jiragen sama a Rasha

Rahotanni daga Moscow babban birnin kasar Rasha, na nuni da cewa an samu fashewar Bam a filin saukar jiragen sama na Domodedovo, inda ake kyautata zaton cewa mutane 31 sun mutu sanadiyyar fashewar bam din.

Har wau yau rahotanni na cewa mutane 100 sun jikkata sanadiyar harin wanda ake ganin dan kunnar bakin wake ne ya fasa bam din.

Babban mai binciken laifuka na kasar Rasha ya ce 'yan ta'ada ne suka kai harin, a yayinda shi kuma shugaban kasar Dmitry Medvedev ya ce kasar za ta tabbatar da kama wadanda suka gudanarda harin.

Filin saukan jiragen saman na wajen kilimota 40 daga cikin garin na Moscow.

A kodayaushe dai filin saukar jiragen saman na cike da baki daga kasashen waje da kuma masu yawon bude ido.

'Yan sanda sun tsaurara matakan tsaro a filayen jiragen saman dake fadin kasar.