Ma'ikatan rajistar zabe sun koka kan rashin biyansu alawus

A Najeriya, wasu masu aikin yi wa kasa hidima wato 'yan NYSC wadanda ke aikin rajistar sunayen masu kada kuri'a a jihar Enugu, sun koka bisa rashin biyansu kudaden alawus din da aka alkawarta masu,duk kuwa da labarin da suka ce sun samu cewa, hukumar zabe ta samar da wadannan kudade.

Haka batun yake a wasu sassa na kasar inda masu aikin yiwa kasa hidimar ke kokawa. Hasali ma a Talatar nan wasu daga cikin masu yiwa kasa hidimar a jihar Enugu sun ce ba za su ci gaba da aikin ba har sai an biya su hakkokinsu.

Har misalin karfe daya na ranar, ba a kai ga fara aikin ba a wasu rumfunan yin rajistar.

Sai dai wani babban jami'in hukumar kula da masu yiwa klasa hidima a jihar ya ce ana kokarin a biya su kudaden nasu.

Masu aikin yi wa kasa hidimar da ke wannan korafi, sun ce suna yin iya bakin kokarinsu, don ganin aikin sabunta kundin sunayen masu kada kuri'ar da aka dauke su a kai, yana gudana kamar yadda ya kamata a jihar Enugu.

Sai dai sun ce suna yin hakan ne cikin mawuyacin hali, a cewar daya daga cikin masu aikin rajistar, wadda ba ta so a ambaci sunanta ba;

"Ta fuskar kudi kam, a gaskiya muna jin jiki. Saboda muna ta aiki tun daga ranar da aka fara wannan aiki, kuma akasarinmu nesa muke zaune. Mafi yawancin lokuta ma sai mun karbi rancen kudi mu zo wurin aiki. Galibi da yunwa muke yini muna aiki."

'Ba'a biya mu kudin alawus din makamar aiki ba'

Wani mai aikin yiwa kasa hidima da wannan matsala ta shafa, wanda shi ma ba ya so a ambaci sunansa, ya yi karin bayani game da matsalar da suke fuskanta; "Ba a biya mu kudin alawus dinmu na koya mana makamar aiki ba, ba kudin mota na zuwa wurin aiki da na abinci. Kai ba a biya mu komai ba."

"Idan har sai a karshen aikin za a biya mu, ya kamata a sanar da mu. Idan kuma a wannan makon da muke ciki za a biya mu, to mu sani. Kar su bar mu cikin duhu." Damuwar matasan da ke aikin rajistar ta kara habaka ne, bayan da suka ji duriyar labari cewa, hukumar zabe ta kasa, ta mika kudaden alawus din nasu ga sakatariyar hukumar kula da masu yi wa kasa hidima ta jihar Enugu, amma kuma suka ji shiru. Don haka na nemi jin ta bakin Mista Aniefiok Okpong-ete, babban jami'in hukumar ta NYSC a jihar Enugu, ya kuma shaida mani cewa, an kammala bin matakan biyan matasan da ke aikin rajistar, kudi naira dubu goma sha tara da dari shida kowannensu, a matsayin wani bangare na hakkokin nasu. "Matsalar tsaikon biyan ta taso ne sakamakon azarbabin da hukumar zabe ta yi, na yayata labarin aiko mana da kudaden, amma kuma a lokacin kudin ba su kai ga shiga hannunmu ba." In ji Mista Aniefiok Okpong-ete

Mista Aniefiok Okpong-ete ya kara da cewa, bayan an kammala aikin rajistar kuma, za a biya su cikon dubu ashirin-ashirin, kamar yadda aka alkawarta masu.