Shugaba Karzai zai kaddamar da 'yan majalisar kasar

Image caption Shugaba Karzai

Shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai zai kaddamar da 'yan majalisun dokokin kasar, abinda zai kawo karshen kiki kakar da ta so rarraba kawunan 'yan siyasar kasar.

Wannan dai ya biyo bayan korafe korafen da aka dade ana yi kan cewa zabukan na cike da magudi.

Mista Karzai ya so jinkirta bude majalisar da akalla wata guda domin kyale kotun sauraren kararrakin zabe ta kammala aikinta.

Yayinda su kuma zababbun 'yan majalisar suka bayyana wannan a matsayin wata alama a bangarensa na soke wasu daga cikin kujerun da 'yan adawarsa suka samu.

Sai dai kuma kasashen duniya sun yi na'am da sabbin 'yan majalisun, musamman ma kasashen yammaci wadanda ke dari darin kada wannan fito na fiton da suke yi a tsakaninsu ya haddasa tashin hankali akan titunan kasar.

Shi dai shugaba Karzai ya yi Allah wadai da abinda ya kira yunkurin da baki ke son yi na haddasa fitina a Afghanistan ta hanyar marawa 'yan majalisun baya.