Dangin Yar 'adua sun fice daga PDP

Yayinda babban zaben kasa baki daya ke kara karatowa a Najeriya, jam'iyyar PDP mai jan ragamar mulkin kasar ta samu wani babban koma-baya a jihar Katsina.

Wani rahoto da muka samu ya ce Jam'iyyar CPC a yanzu haka tana can tana shagulgulan karbar 'Yan uwan Marigayi Shugaba Ummaru 'Yar adua.

A wani taron manema labarai ne dazu-dazun nan, Yayye da Kannen Marigayi 'Yar aduan suka tabbatar da ficewarsu daga Jam'iyyar PDP inda suka tsunduma zuwa CPC.