Barkewar cutar kwalara a Ghana

Taswirar kasar Ghana
Image caption Cutar kwalara ta barke a Ghana

Hukumar lafiya ta kasar Ghana ta ce an samu barkewar cutar amai da gudawa a wasu sassan kasar.

Hukumar ta ce tuni cutar ta hallaka mutane biyu, yayin da wasu mutanen fiye da hamsin ke karbar magani a wasu asibitocin kasar.

A wata hira da ya yi da manema labarai a birnin Accra, shugaban hukumar lafiya ta Ghanan, Dakta Elias Sory ya ce koda yake wadanda cutar ta hallaka ba su da yawa, lamarin ya kai inda za'a bayyana shi a matsayin annoba.

Ya ce jihohin da cutar ta fi shafa su ne Accra, da kuma jihar tsakiyar kasar.

Dakta Elias ya ce hukumarsa ta bayar da umarni ga daraktocin kiwon lafiyar kasar da ke jihohi da su dauki matakan magance yaduwar cutar.