Mutanen Masar sun yi zanga zanga game da shugabancin Hosni Mubarak

'Yan sandan kwantar da tarzoma sun yi harba hayaki mai sa hawaye, sun kuma rika feshin ruwa ga masu zanga zangar nuna kyamar gwamnati a Alkahira, babban birnin Masar.

Dubban masu zanga zanga dake koyi da tarzomar da aka yi a Tunisia ne suka rika rera wakokin la'antar shugaba Hosni Mubarak, suka kuma rika jifar 'yan sanda da duwatsu.

An rika artabu tsakanin masu zanga zangar da 'yan sanda a kan tituna, lokacin da suka yi kokarin hana zanga zangar a majalisar dokoki.