Wasu 'yan takara sun kulla kawance a Nijar

Malam Seini Omar
Image caption Daya daga cikin 'yan takara shidda da suka kulla kawancen

A Jamhuriyar Niger, wasu yan takara shidda a zaben shugaban kasar da zaa yi ranar litinin mai zuwa sun kulla wani sabon kawance domin marawa daya daga cikinsu baya, idan har zaben ya kai ga sai an yi zagaye na biyu.

Yan takarar da suka kulla wannan yarjjeniya sun hada da tsohon shugaban kasa Alhaji Mahamane Ousmane na Jam'iyyar CDS Rahama da tsohon prime Minista Hamma Amadou na Moden-Lumana da kuma Malam, Seini Oumarou na MNSD -Nasara.

An yiwa sabon kawancen lakanin, ARN, Hadin kan yan kasa, kuma tuni har yan takarar sun amince su marawa junansu baya a zaben 'yan majalisar dokoki, a wuraren da ba su tsayar da nasu yan takarar ba.