Obama ya ce 'yan siyasa su yi aiki tare

Image caption Shugaba Obama

A Jawabin Shugaba Obama kan halin da Amurka ke ciki ya yi kira 'yan majalisun dokokin kasar na jam'iyyu dabam-daban da su hada kai su yi aiki tare.

Yace sababbin dokoki za su iya nasara ne kurum idan har 'yan jam'iyyun Democrat da Republican sun ba shi goyon baya.

Inda ya yi misali da cewa za su cigaba ne tare ko kuma su makale a wuri guda, saboda kalubalen da ke fuskantar su ya zarta jam'iyya ko siyasa.

A wata alama ta nuna kudirin aiki tare, 'yan jam'iyyun biyu sun zauna ne a gwamutse da juna lokacin da ya ke jawabin maimakon zama a bangarori dabam na zauren majalisar.

'Yan majalisar dai sun yi ta sowa da tafi lokacin jawabin na sa amma martanin da jam'iyyar Republican ta mayar bayan jawabin ya soki abinda suka kira yawan kashe kudi da ba zai iya dorewa ba da gwamnatin Obaman ke yi.