An dora alhakin tashin bam a Rasha kan matsalar tsaro

Wadansu mutane da harin bam din Rasha ya shafa

An dora alhakin tashin bam din kunar- bakin- wake da aka kai a babban filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Moscow, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 35 akan rashin isasshen tsaro.

Kakakin sashen musamman na yaki da ta'addanci a Rasha, Nikolai Sintsov ne ya furta hakan.

Tuni dai wannan lamari ya tilastawa shugaban kasar Rasha, Dmitry Medvedev soke ziyarar da ya shirya yi zuwa birnin Davos, kana ya bayar da umarnin a tsaurara tsaro a tashoshin jiragen sama da na kasa.

Masu bincike na Rasha sun ce wani dan kunar-bakin-wake ne ya tayar da bam din a harabar filin jirgin sama na Domode-dovo.