Ambaliya: Australia ta bullo da harajin wucin gadi

Firaministar Australia Julia Gillard
Image caption Ana bukatar dala biliyan 5 domin sake gina garuruwa da tsugunar da wadanda ambaliyar ta tarwatsa

Gwamnatin Australia ta sanar da wani sabon haraji na wucin gadi domin tallafawa wajen sake gina jihohin da ambaliya ta shafa.

Firaministar Australia Julia Gillard ta ce "a yau na sanar da wani shirin haraji da rage kashe kudin gwamnati da zai samar da fiye da dala biliyan biyar da rabi domin sake gina wuraren da ambaliyar ruwa ta lalata".

Sai dai ta ce wadanda ke samun kasa da dala dubu hamsin a shekara da kuma wadanda ambaliyar ta rutsa da su, ba za su biya harajin ba.

Gwamantin Australia ta kwatanta mummunar ambaliyatr ta kwanan nan da bala'i mafi tsada da ya taba afukuwa a tarihin kasar.

Kuma tana bukatar dala biliyan 5 domin sake gina garuruwa da tsugunar da wadanda ambaliyar ta tarwatsa.

Fira minista Julia Gillard ta ce rancen kudi zai kara jefa kasar cikin bashi don haka ba zabi ba ne mai kyau a wajenta, a don haka ta bullo da karbar haraji na wucin gadi.