BBC za ta rage ma'aikata 650

Peter Horrocks
Image caption Shugaban bangaren watsa shirye-shirye ga kasashen waje na BBC Peter Horrocks

Bangaren BBC mai watsa shirye-shirye ga kasashen waje ya bada sanarwar cewa zai rage sama da rubu'in yawan ma'aikatansa, cikin shekaru uku masu zuwa, tare da soke wasu shirye shirye, da ma watsa shirye-shiryen cikin wasu harsunan.

Shugaban bangaren watsa shirye-shiryen ga kasashen waje, Peter Horrocks ya ce an dauki matakin ne a sakamakon rage kudaden da gwamnati ke baiwa hukumar. Ya ce mun dauki dukkan matakin da zamu iya, mun bayyanawa ma'aikatar kasashen waje irin tasirin sauye-sauyen da muka bada sanarwa a yau.

A ranar Talata ma an bada sanarwar rufe sassa biyar masu watsa shirye shirye cikin wasu harsuna.

Ra'ayin kungiyar 'yan jaridu

Sai dai kuma kungiyar 'yan jaridu ta ce zabtarewar da aka yi za ta yi matukar illa ga bukatun Burtaniya a kasashen duniya.

Baicin rufe sassanta biyar masu watsa shirye-shirye a cikin harsuna daban-daban na duniya daga cikin sassa talatin da biyu da take da su, wadanda suka hadar da na Albania, Sabiya, Macedoniya, Harshen portugese ga mutan Afrika, da kuma shirye-shiryen Ingilishi ga mutanen yankin Caribean.

Image caption BBC na da kima sosai a idon masu saurarenta

BBC za ta daina watsa shirye-shirye ta hanyar Radio a cikin harsuna bakwai, wadanda suka hadar da Rashanci, harshen Mandarin na kasar Sin, da harshen Turkey, da kuma sashen da ke watsa shirye-shiryensa a harshen kasar Yukrain.

Hakazalika BBCn za ta dakatar da watsa shirye-shiryenta ta hanyar gajeren zango a wasu karin harsunan guda shida da suka kunshi na Hindu, Indonisiya, da Swahili.

'Suna ganin sashen da kima'

Sannan za a rage adadin shirye-shiryen da ake watsa wa da harshen Turanci. Shirye-shiryen radiyo guda uku da suka fi shahara a harshen Rasha a yanzu za a koma watsa su ne ta hanyar Intanet kawai, sai dai sashen na Rasha zai sallami kusan rabin ma'aikatansa.

BBC Hausa

Bangaren BBC mai watsa shirye-shirye ga kasashen waje ya bada sanarwar cewa zai rage kudaden da yake kashewa ta hanyar sauye-sauye. Tasirin hakan a kan BBC Hausa, shi ne ana bukatar ta rage kudaden da take kashewa da kashi 10% cikin dari nan da shekaru uku masu zuwa. Wannan ka iya haifar da sauye-sauye ta fuskar ma'aikata, yanayi da kuma lokutan watsa shirye-shirye, amma babu wata illla da hakan zai haifar nan take sakamakon sanarwar da aka bayyana a ranar 26 ga wannan watan Janairu 2011.

Peter Horrocks, ya ce ana bukatar wadannan sauye-sauye ne, saboda gagarumin raguwar da aka samu a yawan kudaden da gwamnatin Burtaniya ke baiwa BBC don gudanar da aikace-aikacenta.

"Sashen na BBC an kafa shi ne don samar da aikace-aikacensa ga duniya, kuma mun sani daga martanin da muke samu daga masu sauraronmu a sassan duniya cewa, suna ganin sashen da kima.

"Duk da cewa muna takaicin wadannan sauye-sauyen da za mu yi, hakan ya zama dole domin mu cike gibin raguwar da muka samu a kudaden shigarmu," a cewar Peter Horrocks

Gabaki daya dai ma'aikata dari shida da hamsin ne za su rasa ayyukansu a tsawon shekaru uku masu zuwa, kwatankwacin rubu'in ma'akatan da ake da su a halin yanzu.

BBC ta kuma kara da cewa, tana hasashen masu kallo, sauraro ko karanta labaranta na sashen nata mai watsa shirye-shiryensa ga kasashen duniya za su iya raguwa da kimanin miliyan talatin a mako, wato daga cikin jimillar masu sauraro miliyan 180 da ake da su a yanzu zuwa miliyan 150.

Sir John Tusa, wani tsohon shugaban sashen na BBc mai watsa shirye-shiryensa ga kasashen duniya, ya ce wadannan yanke-yanken abin kaico ne ga masu sauraro da kuma manufofin harkokin waje na Burtaniya.

Kuma babban abin alhini ga sashen na BBC mai watsa shirye-shiryensa ga kasashen duniya.