Yiwuwar ci gaba da zanga-zanga a Masar

Yiwuwar ci gaba da zanga-zanga a Masar
Image caption 'Yan sanda sun yi amfani da ruwa da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar

Mahukuntan Masar na shirin tunkarar yini na uku na zanga-zangar rashin amincewa da gwamnati, inda aka kame daruruwan masu jerin gwano.

Masu zanga-zanga a biranen kasar da dama dai sun ci gaba da jerin gwanon nuna adawa da gwamnati duk da gargadin da mahukunta su ka yi musu kar su yi.

An samu rahotannin mutawar karin mutane biyu sai dai ba'a hakikance ko su na da dangantaka da zanga-zangar ba.

A alkahira, babban birnin kasar, 'yan sandan kwantar da tarzoma sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye a fafatawar da suka yi da dubunnan masu zanga-zanga.

A garin Suez da ke Gabashin kasar kuwa, masu zanga-zangar sun cinnawa wani ginin gwamnati wuta.

Jama'a za su kuma bazama

Rahotanni sun ce matakan da 'yan sanda su ka dauka ne suka kara iza wutar rikicin kodas ya ke jakadan Masar a Burtaniya, Hatem Seif El Nasr ya musanta zargin.

Yace " 'yan sanda sun yi matukar taka-tsan-tsan kuma sun yi amfani da bututun ruwa wurin tarwatsa zanga-zangar ne bayan da wuri ya kure musu, amma ba na zaton hakan ya jikkata kowa.

Ana saran jama'a za su kuma bazama kan tituna domin ci gaba da zanga-zangar adawa da gwamnati, abinda ke nuna akwai sauran kalubale a gaban mahukuntan kasar.

A ranar Laraba dai ba a samu wani gangami mai girman wanda aka samu a ranar Talata ba, sai dai jama'a sun ci gaba da hallara rukuni-rukuni ta hanyoyin da su ka ga dama, abinda kuma ke tayarwa da gwamnati hankali.

Tunda farko ministan cikin gida na kasar ya bada sanarwar haramta dukkan wata zanga-zanga.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hilary Clinton ta nemi mahukuntar Masar da kada su hana zanga-zangar limana ko su toshe hanyoyin sadarwa ciki ko har da na zumunta da musayar ra'ayi.