Rijistar masu zabe: INEC ta nemi a kara mata mako guda

Rijistar masu zabe: INEC ta nemi a kara mata mako guda
Image caption Da farko dai an samu matsala sosai a wurin aikin rijistar

Shugaban Hukumar zabe ta Najeriya Farfesa Attahiru Jega, ya nemi a kara masa mako guda domin kammala aikin rijistar masu zaben da ke gudana.

Attahiru Jega ya gaya wa Majalisar Datawan kasar cewa, karin mako guda zai ishi Hukumar ta kammala rijistar dukkan wadanda su ka cancanci a yiwa rijistar.

Kimanin mutane miliyan 70 ne dai ake saran za a yiwa rijistar domin samun damar kada kuri'a.

Ana gudanar da aikin rijistar ne a wurare dubu 120 a fadin kasar. Kuma ana saran kammala aikin ne a ranar Asabar mai zuwa.

Majalisar Wakilai ta kasar ta amince da gyara dokar zaben a ranar Talata, wacce za ta bada karin lokaci domin kammala aikin rijistar.

Sai dai dokar na bukatar amincewar Majalisar Dattawa da kuma sa hannun Shugaba Goodluck Jonathan kafin ta zamo doka.