Interpol na neman tsohon shugaban Tunisia

Tsohon shugaban kasar Tunisia, Zainul Abidina Bin Ali
Image caption Tuni dai Tsohon shugaban Zainul Abidina Bin Ali ya tsere zuwa kasar Saudiyya

Hukumar 'yan sanda ta kasa da kasa, Interpol ta bada sammacin kama hambararren shugaban kasar Tunisia, Zainul Abidina Bin Ali da shida daga cikin iyalansa.

Interpol ta ce ta bukaci kasashen da ke da wakilci a cikinta da su cafke Mr. Bin Ali, wanda ya tsere zuwa Saudi Arebiya bayan da zanga-zanga ta barke a Tunisia farkon watan nan.

Interpol ta dauki wannan matakin ne bayan da sabuwar gwamnatin Tunisia ta zargi Mr. Bin Ali da mallakar dukiya ta haramtacciyar hanya tare da taskance kudade a kasashen ketare.

Tuni dai kasar Faransa ta bada umarnin tsare duk wata dukiya da Ben Ali da iyalansa su ka mallaka.