Majalisar Dattijan Najeriya ta kara wa'adin rajistar zabe

A Najeriya, Majalisar Dattijan kasar ta kara wa'adin rajistar masu kada kuri'a da kwanaki talata bayan da Hukumar zaben kasar ta nemi da a kara mata mako guda, domin kammala aikin rajistar.

Majalisar ta kara kwanakin ne bayan da ta gayyaci shugaban hukumar zabe, Farfesa Attahiru Jega da ya hallara a gabatan domin ya yi mata bayani game da wasu matsalolin da ake fuskanta wajen aikin rajistar a yayinda wa'adin da aka dibarwa shirin zai cika a ranar asabar mai zuwa.

Farfesa Jega dai ya kwashe wajen sa'o'i hudu yana amsa tambayoyi daga 'yan majalisar, kan irin matsalolin da ake fuskanta na aikin rajista, wanda suka hada da rashin isashen na'urar yin rajista da tawadar gurza rubutun katin zabe da dai sauran su.

Shugaban Hukumar dai ya dau lokaci yana bayani daya bayan daya kan kokarin da hukumar ke yi domin magance matsalolin, a inda kuma ya bukaci 'yan majalisar da su gyara dokar zabe da mako guda domin karawa hukumar lokacin kammala aikin rajistar.

Baya bayanan nasa ne da kuma bukatar daya gabatar, Majalisar ta amince da gyaran dokar zaben inda ta ba hukumar damar kammala aikin rajista daga kwanaki sittin kafin ranar zabe, zuwa kwanaki talatin.

Senata Ahmed Lawal, dan majalisa ne a majalisar dattawan Najeriya, kuma ya shaidawa BBC cewar 'yan majalisar sun bawa hukumar sahawarar kara sa'ido a matakan yin rajistar, domin magance irin matsalolin da ake fuskanta.

Ya zuwa yanzu dai hukumar zaben ta ce ta kammala rajistar masu kada kuri'a sama da miliyan ashirin da takwas cikin masu zabe miliyan saba'in da aka kyautata zaton kasar na da su.

Ajiya ne dai Majalisar Wakilai kasar ita ma ta amince da gyaran dokar zaben, wacce ta bada karin kwanaki talatin domin kammala aikin rijistar. Abin jira a gani shine ko hukumar zaben za ta iya kamala aikin rajistar cikin kwanakin da aka kara mata a dokar zabe.

Karin bayani