An bada sammacen damke Ben Ali

Zine Al-abdine Ben Ali
Image caption Zine Al-abdine Ben Ali

Gwamnatin Tunisia ta bada sammacin na kama tsohon shugaban kasar, Zine al-Abidine Ben Ali a duk inda ya ke a duniya.

Ma'akatar shari'a ta kasar ta ce ta bukaci hukumar Interpol ta taimaka mata wajen kama shi da kuma wasu danginsa da suka hada da uwargidansa, Leila Trabelsi.

Ana nemansu ne bisa zargin tara dukiya ta haramtacciyar hanya da kuma kwasar dukiya a fitar da ita waje, ba bisa ka'ida ba.

Mr Ben Ali da kuma wasu daga cikin danginsa sun tsere ne zuwa Saudiyya bayan zanga zangar da jamaa suka yi ta nuna kyamar gwamnati a farkon wannan watan.