Korea ta Kudu ta fara gina wasu gidaje dubu talatin a Ghana

Shugaba John Atta Milss na Ghana
Image caption Shugaba John Atta Milss na Ghana

Yau ne shugaba John Atta Mills na Ghana ya aza harsashin gina gidaje dubu talatin a birnin Accra don anfanin jami'an tsaron kasar da suka hada da 'yan sanda da sojoji da sauransu.

Aikin wanda zai ci kudi sama da Dollan Amurka milliyon dubu guda da rabi shi ne kashin farko na gidaje dubu dari biyu da gwamnatin Korea ta Kudu za ta gina don anfanin al'ummar kasar.

Wadanda suka halarci bikin aza harsahin dai sun hada da ministoti da manyan jami'an gwamnatin Ghana da kuma ministan mahallin Korea ta Kudun.