'Shugabanci na gari ne kawai shi zai kauda tashin hankali a Afrika'

Image caption Mahalarta taron laccar jaridar Daily Trust

A Najeriya, mahalarta wata laccar da jaridar Daily Trust ta shirya a Abuja sun bayyana cewa zai yi wuya kasashen nahiyar Afirka da dama su kauce wa rigingimun da ke faruwa a wasu kasashe irin su Tunisia da Masar sai shugabanni sun sauya salon jagoranci ta hanyar kamanta adalci da gaskiya.

Masanan dai sun ce wajibi ne shugabanni su kyale al`umomi su zaba wa kansu wadanda suke so su shugabance su kafin a samu zaman lafiya.

Laccar wadda aka yi wa lakabi da kalubalen da ke fuskantar shugabanci nagari a nahiyar Afirka ta samu halartar wasu fitattun shugabannin al`umma, irin su tsohon shugaban kungiyar tarayyar Afirka, Salim Ahmed Salim, da tsofaffin shugabannin Najeriya, janar Yakubu Gawon da janar Muhammadu Buhari masu ritaya, da kuma wasu masana.

Mahalartar taron dai sun bayyana cewa cin hanci da rashawa su ne ummulhaba`isin ci bayan da suka ce mafi yawan kasashen nahiyar Afrika ke fuskanta duk kuwa da dimbin albarkatun da suke da su.

Matsalar Shugabanci a Afrika

Image caption Janar Yakubu Gowon

Tsohon shugaban Najeriya Janar Yakubu Gowan mai ritaya ya ce irin yadda iko ke baiwa shugabanni a nahiyar damar wawurar dukiyar kasa na daga cikin matsalolin da kan sa irin wadannan shugabannin kin sauka daga karagar mulki idan wa`adinsu ya kare.

Ya ce waji bi ne a sake lale idan ana so a kai labari; "Hanya daya da nahiyar Afirka za ta ci gaba ita ce idan masu mulki da kuma wadanda ake mulka za su mai da hankali wajen kyautata walwala da ci gaban al`uma." General Yakubu Gowon.

"Kuma ina tabbatar muku da cewa za su samu gagarumin ci gaba idan shugabanni suka kasance masu tsoron Allah, kana mabiyansu suka kasance masu sa-ido a kansu don tabbatar da cewa sun aikata kamata."

Ita kuwa, Mis Arunma Oteh, wadda ta gabatar da kasida a wajen taron gargadi ta yi cewa wata guguwar sauyi ta fara kadawa a nahiyar Afirka a kasashe irin su Tunisia da Masar, kuma ba makawa za bazama zuwa wasu kasashen nahiyar muddin shugabanni ba su bai wa jama`a damar zaba wa kansu shugabanni ba.

'An tauye hankin jama'a'

"Mafi yawan `yan Afirka an tauye musu `yancinsu a siyasance. Don haka wajibi ne a bari jama`a su dinga zaba wa kansu shugabanni, idan ba haka za a yi fama da rigingimu."

Ta kara da cewa irin ci gaban da duniya ke samu ta fuskar fasahar sadarwa da ta sanya kan jama`a na kare wayewa. Don haka irin kama-karyar da aka yi a baya talakawa suka jure, da wuya al`ummomin wannan zamanin su iya jurewa.

Wannan dai ba shi karon farko da ake fito da ire-iren matsalolin da ke tarnaki ga harkar shugabanni a nahiyar Afirka ba, kuma maimakon a samu ci gaba masu lura da la`amura na nuna cewa lamarin sai kara tabarbarewa yake yi.

Shugaban gidauniyar inganta shugabanci a nahiyar Afirka ta Mo Ibrahim Foundation, wato Dr Mo Ibrahim na daga cikin wadanda aka sa-ran zai gabatar da kasida a wajen taron, amma bai samu damar yi ba, duk da cewa ya iso Najeriyar sakamon zazzabin cizon sauro da ya buge shi kamar yadda aka sanar a wurin taron.