Kungiyar Human Rights Watch ta fitar da rahoto kan Jos

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Wani rohoto da kungiyar kare hakkin bil 'adama ta Human Rights Watch ta fitar akan rikicin Jihar Plateau a Najeriya na cewa kimanin mutane dari biyu ne aka kashe daga watan Decembar shekarar 2010 zuwa yau.

Kungiyar ta ce an kashe mutanen ne a yunkurin daukar fansa.

Ta dai kara da cewa cikin wadanda aka kashe din har da yara kanana.

Kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnati da ta yunkura wajen kare fararen hula, tare da barin mai baiwa sakatare janar na majalisar dinkin duniya shawara akan kisan kare dangi wato Francis Deng, ya ziyarci Jihar ta Plateau.