Masu dakon mai a Najeriya za su fara yajin aiki

A Najeriya, Kungiyar masu motocin dakon mai ta kasar wato NARTO ta yi barazanar fara yajin aiki idan gwamnatin kasar ta ki rage kudin man diesel da manyan motocin ke amfani da shi.

Kungiyar ta ce ba ta cin wata riba a harkar dakon mai sakamakon tsadar mai a da shirin gwamnati na janye hannu daga harkar mai ya haifar.

Don haka kungiyar ta yi kira ga gwamnati ko ta janye shirin ko kuma ta kammala aiwatar da shi ta yadda zai shafi kowa da kowa.

Kungiyar ta kara da gargadin muddin ba'a dauki mataki daya cikin biyun ba, nan da makonni biyu, to za ta fara yajin aikin sai baba ta gani.