Mutane kusan dubu hudu sun yi gudun hijira daga garin Tafawa Balewa

Kungiyar agaji ta Red Cross ta bayyana cewa yanzu haka akwai 'yan gudun hijira kusan dubu hudu wadanda suka tsere daga tashin hankalin da aka yi a garin Tafawa Balewa dake Jihar Bauchi a Nijeriya.

Kungiyar ta ce 'yan gudun hijirar, wadanda suka hada da mata da kananan yara, na matukar bukatar kayayyakin taimako.

Tashin hankalin na Tafawa Balewa ya barke ne sakamakon wani sabani tsakanin wasu matasa, kan wasan kwallon Snooker.

Rundunar yansandan jihar ta ce ta kama wasu mutane da take zargi, wadanda ta same su da makamai.