Shugaba Mubarak ya rushe majalisar ministocinsa

Hakkin mallakar hoto AFP

Shugaban Masar Hosni Mubarak ya rushe majalisar ministocinsa tare da alkawarin kawo sauye-sauyen dimokradiyya da tattalin arziki.

Wannan dai wani martani ne da ya mayar ga zanga zangar da ta barke a kasar a jiya Juma'a.

Shugaba Mubarak a yayin wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin din kasar ya bayyana ne cikin yanayi na kamala cike da kudurin tabbatar da kawo karshen wannan tashin hankalin da bai taba fuskantar irinsa ba a iya tsawon shekarun talatin din da ya yi akan kujerar mulki.

Shugaban ya ce ya aminta cewar bukatar masu zanga zangar ba ta saba doka ba.

Sai dai ya zarge su ne da taso da tashin hankali domin jefa kasar Masar cikin wani yanayi.

Wasu dai na ganin wannan jawabin na iya sake hasala mutanen, ta yadda za su ci gaba da kalubalantar sa fiye ma da yadda suka yi a baya.

Shi dai Mr. Mubarak ya kare aiyukan da gwamnatinsa ta yi ne, wani batu kuma da shi ne ya janyo rashin tabbaci tare da jefa shakku a zukatan daruruwan al'ummar da suka fito kan tituna domin nuna adawarsu akai.

Ya dai yi musu alkawarin ci gaba da sauye sauye ta fuskar demokradiyya, amma a iya sanin su masu adawa da shi din, wannan ba sabon al'amari bane. Batu ne da suka sha jinsa daga bakinsa.

Sai dai ya dauki wani gagarumin mataki na sallamar majalisar ministocinsa.

Tambayar ita ce shin wannan ya isa ya sanya masu zanga zangar su saduda, ko kuwa shine zai kasance musu wani mataki na ci gaba da matsawa kan yi musu abinda ya fi haka?