Obama ya ce kada Masar ta yi amfani da karfin soji

Hakkin mallakar hoto AFP

Shugaba Barack Obama na Amurka yayi kira ga jami'an kasar Masar kada su yi amfani da karfi wajen kwantar da zanga zangar da ake yi a kasar.

Mista Obama ya bukaci Husni Mubarak ya dauki kwararan matakai wajen kare hakkokin bil adama, tare da bada damar shiga shafukan yanar gizo ko amfani da wayar tafi da gidan ka.

Shugabannin biyu sun tattauna ne da juna a karo na farko tun bayan da aka fara zanga zangar.

Mista Obama shaidawa Mista Mubarak cewa nauyin na al'ummar kasar ya rataya a awuyansa, don haka ya kamata ya baiwa demokradiyya da 'yan cin bayyana ra'ayi karin mahimmanci.