An sabunta: 17 ga Janairu, 2012 - An wallafa a 15:21 GMT

Mandela: Yaki da cutar Aids

Nelson Mandela

Nelson Mandela ya taka rawa wajen yaki da cutar Aids

Nelson Mandela ya taka rawa sosai wajen yakar cutar HIV da kuma AIDS a Afrika ta Kudu wacce ke kan gaba wajen fama da cutar.

A lokacin da aka sallame shi daga gidan yari, cutar Aids ba ta bayyana sosai a kasar ba.

Amma bayan ya bar mulki a 1999, Mr Mandela ya yi yaki da cutar ta fannoni da dama ciki har da wayar da kan jama'a a kan cutar da kuma neman samar da cikakken magani.

Sai dai ba kowa ba ne ya ke bayyana cutar a bainar jama'a.

A shekara ta 2005, Mr Mandela ya ba da mamaki inda ya bayyana cewa dansa Makgatho, ya mutu ne saboda cutar ta kanjamau.

Ya nemi jama'a da su dinga zancen cutar a bainar jama'a "domin ta zama cuta ta yau da gobe".

Rikicin jam'iyyar ANC

Afrika ta Kudu ce kasar da ta fi kowacce yawan masu fama da cutar HIV.

Ana kallon talauci a matsayin abubuwan da suka haifar da yaduwar cutar da matsalar zirga-zirgar baki.

Tun bayan hawanta mulki jam'iyyar ANC, ta mayar da hankali wajen gano bakin zaren cutar ta Aids.

A baya gwamantin kasar ba ta maida hankali wajen samar da magungunan cutar ba, sai dai hakan ya sauya tun bayan zuwan Jacob Zuma.

A ranar bikin cutar Aids ta shekara ta 2000, Mandela ya bayyana cewa: "kasar mu na fuskantar mummunar matsala daga cutar HIV.

"Muna fuskantar wata babbar abokiyar gaba wacce ta ke aboye, kuma tana barazana ga rayuwar jama'armu".

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.