An sallami Nelson Mandela daga asibiti

An sallami Nelson Mandela daga asibiti Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nelson Mandela ya taka rawa sosai wajen yakar wariyar launin fata a Afrika ta Kudu

An sallami tsohon shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela daga asibiti bayan da ya shafe kwanaki biyu ana duba lafiyarsa.

Babban likitan asibitin Vejaynand Ramlakan ya ce Mr Mandela, dan shekaru 92, na fama da cutar da mutane masu shekaru irin nasa ke fama da ita, amma yana cikin koshin lafiya a yanzu.

Mataimakin shugaban kasa Kgalema Motlanthe ya ce "Mandela na cikin koshin lafiya."

Mandela wanda ya taka rawa wajen ceto Afrika ta Kudu, an dauke shi daga birnin Cape Town zuwa Johannesburg a ranar Laraba domin duba lafiyarsa.

A ranar Juma'a Likitocin Mr. Mandela dai sun ce jikin na sa da dama kuma ba ya cikin hatsari sai dai makusantansa na cewa tsohon shugaban kasar mai shekaru 92 ya yi matukar rauni cikin watannin baya-bayan nan.

"A wajen mu yana samun sauki, amma likitoci za su ci gaba da sa ido a kansa," kamar yadda Mr Ramlakan ya shaida wa manema labarai.

Wani rukunin motoci ne ake kyautata zaton sun dauki Mandela daga asibiti zuwa gidansa da ke Houghton wajen birnin Johannesburg.

Masu aiko da rahotanni sun ce ya yi rauni tun bayan da ya daina bayyana a gaban jama'a a shekara ta 2004.

Bayyana ta karshe da ya yi a bainar jama'a ita ce ta lokacin wasan karshe na gasar cin kofin duniya a watan Yulin bara.