An sabunta: 25 ga Fabrairu, 2012 - An wallafa a 13:29 GMT

Mandela: Ya kawo karshen wariyar launin fata

Mandela

Mandela ya jagoranci yaki da wariyar launin fata

Bayan da aka daure shi har tsawon rayuwarsa, Nelson Mandela ya zamo gwarzo a duniya a fagen fafutukar yaki da wariyar launin fata. Amma ya dade yana adawa da banbancin launin fata.

Wariyar launin fata ta samo asali ne tun farkon shugabancin Turawa a Afrika ta Kudu.

Amma ta fara ne bayan da a karon farko jam'iyyar National Party ta hau mulki a 1948, a wani zabe da fararen fata ne kawai suka shiga.

An kafa jam'iyyar ANC a shekarar 1912 domin ta kwato 'yancin Bakake. Mandela ya shiga jam'iyyar a 1942.

Kuma shi da matasa irinsu Walter Sisulu da Oliver Tambo, sun kulla niyyar maida ita jam'iyyar siyasa.
Kwato 'yanci.

A shekarun 1950 Mr Mandela, ya kewaye Afrika ta Kudu domin hada kan mutane wajen nuna adawa da wariyar launin fata.

Bayan da aka zarge shi da wasu laifuffuka, an daure Mandela kafin daga bisani a tsare shi a birnin Johannesburg har tsawon watanni shida.

A 1955, ya jagoranci yaki da wariya inda ya rubuta wa ANC cewa: "Afrika ta Kudu ta kowa ce muddum dai kana zaune a cikinta, Baki ne kai ko Fari."

Shekara guda baya, yana daga cikin masu fafutuka 156 da aka kama ciki har da shugabannin ANC, inda aka zargesu da laifin cin amanar kasa.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.