Zaben Nijar 2011

Hakkin mallakar hoto AFP

Kusan 'yan Nijar miliyan shida ne za su kada kuri'a a ranar 31 ga watan Janairu, domin zaben sabon shugaban kasa.

Zaben zai kafa jamhuriya ta bakwai ne a kasar, bayan da sojin kasar suka hambarar da mulkin farar hula karkashin jagorancin Shugaba Mamadou Tandja a watan Fabrairun shekarar 2010.

Shugaba Mamadou Tandja dai kafin a hambarar da gwamnatinsa ya gudanarda zaben raba gadarma, wanda ya bashi damar kara tsaya wa takarar shugaban kasa a karo na uku.

'Yan takarar Shugaban kasa goma ne suka tsaya neman kuri'un al'ummar kasar a yayinda yawancinsu sun yi aiki da gwamnatoci dabam-dabam da su ka shude a kasar, a yayinda wasu ma sun yi takarar shugaban kasar a baya.

Shugaban Mulkin sojin kasar, Janar Salou Djibo ya kwace mulki ne a watan Fabrairun shekarar 2010, kuma ya tsare tsohon shugaban kasar Mamadou Tandja, saboda gwamnati ta zarge shi da yin sama da fadi da kudaden gwamnatin.

Janar Djibo dai ya yi alkawarin barin kujerar mulki a watan Afrailun bana bayan an kammala zaben watan Janairu.

An dai samu matsaloli wajen shirin zaben, a yayinda hukumar shirya zabe a kasar wato CENI ta fuskanci kalubale a zabukan kananan hukumomi da ta gudanar.

Nijar dai tana fama da talauci da yunwa, amma dai tana da arzikin ma'adanin Uranium.