Shugaba Mubarak ya nada sabon mataimakin shugaban kasa da kuma Pirayim Minista

Shugaba Hosni Mubarak Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Hosni Mubarak na Masar

Bayan kwanaki biyar ana fama da zanga zanga a kan tituna ta nuna rashin amincewa da gwamnati a kasar Masar, Shugaba Mubarak ya nada mataimakin shugaban kasa, sannan kuma ya fara nada sabbin minsitoci.

An ratsad da Mr Omar Sulaiman, wanda tsohon shugaban sashen leken asiri ne na gwamnatin Mr Mubarak a matsayin mataimakin shugaban kasa, yayin da kuma aka nada tsohon shugaban mayakan sama na kasar, Ahmed Shafiq a matsayin Pirayimi minista.

Sakatare Janar na kungiyar Kasashen Larabawa, Mr Amr Moussa, ya ce al'amarin ba a kan wadanda aka nada ba ne, illa a kan irin manufofin da za su gabatar.

Sai dai a Alkhahira babban birnin kasar ta Masar, dubban masu zanga zanga ne har yanzu suke kan titunan kasar inda suke neman da Shugaba Mubarak ya yi murabus.

Masu zanga zangar sun yi ta dauki ba dadi tare da jami'an tsaro a kofar ma'aikatar harkokin cikin gida, an kuma bada rahoton wasu sun jikkata.

A gundumomi da dama dai an ta kwasar ganima a shagunan mutane.

Masu zanga zangar sun bijerewa dokar hana yawon daren da aka fama, to amma har zuwa wannan lokaci rundunar sojojin kasar ba ta tsoma baki ba.