Tattaunawar wasu Jam'iyyun adawa a Najeriya ta cije

Alamar Jam'iyyar adawa ta CPC a Najeriya
Image caption Bisa ga dukkanin alamu tattaunawa tsakanin wasu jami'iyyun adawa a Najeriya na gamuwa da cikas

A Najeriya, bisa ga dukkan alamu tattaunawar da ake yi tsakanin wasu jam'iyyun adawar kasar domin tsayar da dan takara guda da zai tunkari jam'iyyar PDP a zabuka masu zuwa ta cije.

Wasu majiyoyi da ke kusa da tattaunawar da ake yi tsakanin bangarorin biyu sun ce, a yanzu dukkan alamu sun nuna cewa, ba yadda za'a yi bangarorin biyu su sasanta, har ma su tsayar da dan takara daya tsakanin Mallam Nuhu Ribadu na jam'iyyar ACN, da janar Muhammadu Buhari na jam'iyyar CPC, a babban zaben dake tafe.

Dan takarar shugabancin Najeriyar karkashin jam'iyyar ACN, Mallam Nuhu Ribadu, ya shaidawa BBC cewa ba a damawa da shi a tattaunawar da ake yi tsakanin jam'iyyun biyu, inda ya ce hakan na nuni da matsalar da tattaunawar ta ke ciki.

Malam Nuhu Ribadun ya kara da cewa ba a taba kiransa a wannan tattaunawa ba

Sai dai a wata hira da yayi da BBC shi kuwa a kwanakin baya, dan takarar shugabancin Najeriyar karkashin jam'iyyar CPC, janar Muhammadu Buhari ya bayyana cewa tattaunawar da ake yi tsakanin jam'iyyun biyu na nan daram.