Jama'a sun keta dokar hana fitar dare a Masar

Masu zanga zanga a Masar Hakkin mallakar hoto Reuters (audio)
Image caption Masu zanga zanga a Masar

Dubban masu zanga zangar nuna rashin amincewa da gwamnati a Alkahira babban birnin kasar Masar, sun bijerewa dokar hana fitar dare, inda suka fantsama kan tituna, duk kuwa da sabon yunkurin da rundunar sojojin kasar ta Masar ke yi na tabbatar da ikonta.

Masu zanga zangar sun hana wani jerin gwanon tankoki yaki na soji isa dandalin Tahrir.

Wani fitaccen mai yin suka ga gwamnatin kasar Masar din - tsohon Jami'in MDD, Mohammed El-Baradei - ya bi sahun masu zanga zangar da suke dandalin na Tahrir.

El Baradei, wanda kungiyoyin adawa suka bukace shi da ya wakilce su wajen tattaunawa tare da mahukuntan kasar, akan kafa gwamnatin hadin kan kasa, ya shaidawa masu zanga zangar cewa ba ja ba gudu da baya a wannan abu da suka fara.

Ya ce za su cigaba da zanga zangar har sai Shugaba Mubarak ya bar kan karagar mulki.

Wasu 'yan kungiyar 'Yan uwa Musulmi ta kasar Masar - watau kungiyar adawar da ta fi kowacce girma a kasar - su 34 sun tsere daga wani gidan kurkuku.

An ce daga cikin mutanen 34 akwai shugabannin kungiyar.

Sakatariyar harkokin wajen Amirka, Hillary Clinton, ta ce hukumomin Washington na son ganin an shiga wani yanayi na wucin gadi, wanda zai kai ga kafa zababbiyar gwamnati.