Zaman dar dar na karuwa a Masar

Zanga zanga a Masar
Image caption Zanga zanga a Masar

Ana kara samun zaman dar-dar a tsakiyar Alkahira, babban birnin kasar Masar, yayin da masu zanga zanga a fusace suka tinkari wasu tankunan yaki biyu, wadanda suka shiga wani dandali.

Jiragen yaki da helikopta sun rika shawagi kasa-kasa akan dandalin, inda masu zanga zangar nuna kyamar gwamnati suka yi dafifi, a kwana na shidda a jere.

Tun farko a yau, shugaban kasar ta Masar, Hosni Mubarak, ya gana da manyan kwamandojin sa, a ziyarar da ya kai a wata hedkwatar sojojin.

Gidan talabijin din kasar ya ce, shugaban yana sake nazari ne a kan ayyukan tsaro.

Rahotanni sun ce, babbar kungiyar adawar kasar ta 'Yan uwa Musulmi, ta kawo goyon baya ga babban mai sukar gwamnatin Masar din, Mohamed ElBaradei, na ya shiga sasantawa da hukumomin kasar.

Hukumomin Masar din sun kara daukar matakin rage yawan labaran da ake samu game da zanga zangar nuna adawa da su, ta hanyar hana gidan talabijin din Larabci na Al Jazeera watsa shirye shiryensa.

Kasashen duniya kuma sun fara daukar matakan kwashe mutanensu daga Masar.

Gwamnatin Birtaniya na shawartar 'yan kasarta da ba dole bane su cigaba da kasancewa a wasu biranen Masar irinsu Alkahira, Iskandriya da Suez, da su bar wuraren.

Ita kuma Amirka, gobe idan Allah ya kaimu za ta soma kwashe 'yan kasarta da ke Masar, zuwa nahiyar Turai.

Yayin da Turkiyya kuma za ta aika da jiragen sama guda 3 zuwa biranen Alkahira da Iskandariya, domin dauko mutanen ta su 750.

Ya zuwa yanzu dai an yi amunnar cewa, fiye da mutane 100 ne suka hallaka a tashe tashen hankulan da ke faruwa a sassan kasar dabam dabam.

Sakatariyar harkokin wajen Amirka, Hillary Clinton, ta ce hukumomin Washington na son ganin an shiga wani yanayi na wucin gadi, wanda zai kai ga kafa zababbiyar gwamnati.