Amurka ta bukaci gwamnatin Masar ta gudanar da sauyi na siyasa

Kasar Masar Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Gwamnatin kasar Amurka ta nemi Shugaba Hosni Mubarak na kasar Masar daya gudanar da sauyi irin na siyasa a kasar

Gwamnatin Amurka ta fadawa shugaba Hosni Mubarak na kasar Masar cewar yiwa gwamnatin kasarsa garambawul kadai bai wadatar a halin da ake ciki ba.

Bayan kammala wani tsakanninsa da manyan jami'an tsaron Amurka, fadar White House ta nanata kiran da a dau matakin da zai haifar da cikakken sauyi a siyasar kasar ta Masar.

Suma dai shugabannin kasashen Turai sun bada wata sanarwa dake kira ga shugaba Mubarak ya kaucewa zubar da jinin fararen hula, suna masu cewa, dole a baiwa al'ummar kasar Masar hakkinsu na fitowa su bayyana bukatarsu.

Wasu dubun dubatar 'yan kasar Masar dai sun shafe kwanaki biyar suna zanga zangar nuna kyamar gwamnati