Al shabab ta kashe wani mutum bisa leken asiri

Al shabab ta kashe wani mutum bisa leken asiri Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Al-Shabab ce ke da ikon mafi yawancin kasar ta Somalia

Kungiyar al-Shabab ta harbe wani mutum bayan da aka zarge shi da laifin yi wa kungiyar CIA ta Amurka leken asiri.

Ahmed Ali Hussein, mai shekaru 44, an kuma zarge shi da laifin kasance wa mamba a wata kungiyar Islama mai adawa da al-Shabab.

Alkalin al-Shabab ya ce Mr Hussein ya amince cewa ya tallafa wa Amurka a cikin watanni 16 da suka wuce.

Wani dan jarida Mohamed Sheikh Nur ya ce an daure Mr Hussein da sarka, sannan aka harbe shi yayin da aka umarci daruruwan mutane su fito domin kallo.

Mai shari'a Sheikh Omar ya ce Mr Hussein ya amince ya tallafa wa CIA wajen neman bayanai kan wadanda suka shirya harin bom din da aka kai ofisoshin jakadancin Amurka da ke Nairobi and Dar es Salaam wanda ya kashe mutane 224.

Jami'an Amurka sun dade suna zargin al-Shabab da laifin kai hare-haren biyu.