'Yan sanda sun koma kan tituna a Masar

'Yan sanda sun koma kan tituna a Masar Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Mubarak yana gana wa da jami'an gwamnatinsa

'Yan sanda a kasar Masar na komawa wuraren da suka gudu suka bari ranar Juma'a, a sassa daban-daban na birnin Alkahira, lokacin zanga-zangar nuna kyamar gwamnati.

Hukumomin kasar ta Masar sun ce an umarci 'yan sandan su rika aiki tare da sojoji.

Rahotanni na nuna cewa da dama daga cikin masu zanga-zangar har yanzu sun fusata da 'yan sandan kan abin da suka kira, kokarin yin amfani da karfin da ya wuce kima, a yunkurin murkushe zanga-zangar da suke yi.

A yanzu masu zanga-zangar na kira ne da a shiga yajin aikin gama-gari, tare da wani jerin gwano a gobe Talata.

Ministan harkokin cikin gidan kasar ya ce ya bada umarni ga 'yan sandan kasar su yi aiki tare da sojoji.

A birnin Alkahira, jiragen helikwaftan soji na ci gaba da shawagi a sararin samaniyar dandalin Tahrir inda dimbin jama'a suka taru don ci gaba da zanga-zangar kira ga shugaba Mubarak ya sauka daga mulki.

'Gwamnatin Mubarak ta gaza'

Masu zanga-zangar wadanda suka yi kunnen uwar shegu ga dokar hana fita da aka saka, sun ce za su ci gaba da zaman dirshan a dandalin har sai mubarak ya sauka.

Kungiyar nan ta Muslim Brotherhood wadda aka fi sani da Ikhwan na daga cikin wadanda suke goyon bayan zanga-zangar. Muhammad Masry, daya daga cikin shugabannin kungiyar cewa ya yi:

Ya ce: "Gwamnatin Mubarak ta riga ta gaza, mu muna tare da abinda mutane suke goyon baya, muna bukatar sabon tsari, da sabuwar gwamnati, wadda za a gina bisa tsarin demokaradiyya da 'yanci.

Sai dai ya ce kungiyar su ba ta amince da tsohon shugaban Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya Mohammaed Elbaradai a matsayin wanda zai tattauna da gwamnati mai ci a madadinsu ba.

Zanga-zangar da ake yi na kawo damuwa a harkokin kasuwanci a kasar. Bankuna da kasuwannin hada-hadar hannayen jari sun ci gaba da kasancewa a rufe.

Harkokin kasuwanci ma na ci gaba da fuskantar koma bayam sakamakon matakin da gwamnati ta dauka na datse hanyoyin sadarwa na intanet.

Su ma kuma dubban 'yan kasashen wajen da zanga-zangar ta ritsa da su sun fara barin kasar. Kasashen Amurka da Japan da Australia duk sun tura jirage domin debo 'yan kasar su da suka makale a can.

A yanzu dai masu zanga-zanga na kiran da a yi yajin aikin gama-gari don tilasta wa shugaban kasar ta Masar Hosni Mubarak ya yi murabus.