Shugaba Mubarak ya soma daukar matakan tabbatar da ikonsa

Shugaba Hosni Mubarak na kasar Masar
Image caption Shugaba Mubarak na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga masu neman kawo sauyi

Gidan talabijin din kasar Masar ne dai ya karanta wasikar da shugaba Mubarak ya aikewa da sabon Fira Ministansa, Ahme Shafiq.

A cikin wasikar shugaban yayi kira da a gudanar da wasu manufofin tattalin arziki da zasu warwarewa mutane abubuwan dake damunsu.

Ya kuma umarci gwamnatinsa da tayi maganin rashin aikin yi a kasar ta hanyar kirkiro da sabbin guraben ayyuka.

Shugaba Mubarak ya kuma yi magana akan bukatar dake akwai na samun wani cigaba wajen gudanar da wasu sauye sauye a tsarin mulkin kasar dana dokoki, ta hanyar tattaunawa tare da jam'iyyun siyasar kasar.

Sai dai ba wannan bane karo na farko da shugaban yake daukar irin wadannan alkawura a duk lokacin da yaga uwar bari, amma dukkanin alamu na cigaba da nuna cewar canjin da masu zanga zangar kadai zasu kawo a kasar shine na na kawo karshen mulkin Shugaba Mubarak.