An bude rumfunan zabe a Nijar

An bude rumfunan zabe a Nijar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan takara goma ne ke neman mukamin shugaban kasa a zaben

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar sun ce an bude rumfunan zabe a kasar da misalin karfe takwas na safe, domin fara zaben Shugaban kasa da na 'yan Majalisun Dokoki.

Wasu mazauna kasar sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, an bude rumfunan zaben kamar yadda aka tsara a yankunan da su ke.

An shirya wannan zabe ne dai domin bai wa jama'ar kasar damar zaben shugabannin bayan da sojoji suka yi juyin mulki a watan Fabrerun da ya gabata.

Dama dai shugabannin mulkin sojan kasar da suka kifar da gwamnatin Mamadou Tandja, sun yi alkawarin maida ikon kasar hannun farar hula.

Matsaloli

Mutane goma ne dai ke takarar shugabancin kasar karkashin jam'iyyu daban-daban.

Nijar dai na daga cikin kasashen duniya da suka fi fama da talauci, kuma dukkanin jam'iyyun sun tabo batun yaki da talauci a yakin neman zabensu.

Wakilan BBC a jamhuriyar Nijar sun ruwaito cewar tuni wasu tawaggar masu sa ido a kan yadda zaben zai gudana suka isa kasar.

An kuma baza jami'an tsaro a dukkanin rumfunan zaben da ke fadin kasar domin tabbatar da bin doka da oda.

Jama'a da dama suna nuna shakku kan shirin Hukumar zabe ta CENI ganin yadda aka samu matsaloli a zabukan Kananan Hukumomin da aka gudanar.

Sai dai Hukumar ta CENI ta ce ta kimtsa tsaf a wannan karon.

Karin bayani