Tarayyar Afrika ta goyi bayan Kenya kan ICC

Tarayyar Afrika ta goyi bayan Kenya kan ICC Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban Kungiyar Tarayyar Afrika Jean Ping

Tarayyar Afrika ta goyi bayan bukatar Kenya na jinkirta shari'ar da kotun duniya ta ICC ke yi kan wadanda ke da hannun a rikicin da ya biyo bayan zaben kasar.

Kenya ta ce tana bukatar a yi shari'ar mutane shidan da kotun ta ICC ta zarga a cikin gida.

Ta kasa kafa kotun ta cikin gida domin ta binciki rikicin na 2007 - 2008, sai dai ta ce za ta yi hakan yanzu.

A karshen taron da AU ta gudanar, sabon shugabanta, shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema, ya yi watsi da zargin da ake masa na take hakkin bil'adama.

"kasa ta tsarin dimokradiyya ta ke bi. A zaben shugaban kasa mutane na da damar zabar dan takarar da suke so," a cewarsa.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun zarge shi da magudin zabe, muzguna wa 'yan adawa da cin hanci, abinda ya sa suka ce bai cancanci zamowa shugaban kungiyar ta AU.

Kungiyar AU ta kuma kara wa'adin Majalisar Dokokin Somalia da shekara biyu, wanda ke nufin za ta zabi sabuwar gwamnati idan wa'adin wannan ya kare a watan Agusta.