Zanga-zanga mafi girma a Masar

Masu zanga-zanga a Alkahira Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga-zanga a Alkahira

A zanga-zanga mafi girma kawo yanzu a Masar, dubban daruruwan mutane ne suka yi tururuwa zuwa dandanlin Tahrir dake tsakiyar Alkahira, babban birnin kasar domin neman shugaba Mubarak ya sauka daga mulki.

Mazu zanga-zangar sun daga tutocin Masar tare da rera wakokin nuna kishin kasa da kuma na nuna kin jinin shugaba Mubarak.

Manufar dai ita ce a tara mutane miliyan guda. Akwai kuma wata zanga zangar a Iskandiriya, birnin na biyu mafi girma a kasar.

Rahotanni na nuna cewar hadin gwiwar jam'iyyun adawa na siyasa da kuma kungiyoyin addini sun shaida ma gwamnati cewa ba zas u fara tattaunawa da gwamnatin ba ,sai shugaba Mubarak ya sauka daga mulki.

Karin bayani