Gwamnatin Nijeriya ta yi taro kan batun Tsaro a Filato da Borno

Hakkin mallakar hoto AFP

A Najeriya, majalisar tsaron kasar ta kammala wani zama da gwamnonin jihohin Filato da Bauchi da kuma Borno da ke fama da rikice-rikice don nemo hanyoyin magance su.

Dukkan hafsoshin tsaron kasar da kuma sufeto janar na `yan sandan Najeriya sun halarci zaman, wanda aka yi a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja.

Jihohi ukun dai na fama da rikice-rikicen da suka yi sanadiyar asarar rayuka masu yawa a `yan shekarun nan.