A soma kidayar kuri'u a Nijar

Niger 2011 Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan takara goma ne dai suka yi takarar shugaban kasa a zaben na Nijar, yayin da za a zabi 'yan Majalisun dokoki 113

A jamhuriyar Nijar, hukumar zaben kasar na cigaba da tattara sakamakon da aka samu a zaben shugaban kasa da 'yan Majalisar dokoki da aka yi jiya a duk fadin kasar.

Bisa ga dukkan alamu dai an kammala wannan zabe cikin lumana, duk da wasu matsaloli da zaben ya yi karo da su a wasu yankuna.

Sai dai wasu jam'iyyun siyasa na zargin juna da yin makarkashiya yayin zaben. .

Wakilan BBC a fadin kasar ta Nijar, sun ba da rahoton cewa, aikin kidaya kuri'un ya kankama a yankuna daban-daban na fadin kasar.

'Yan takara goma ne dai suka yi takarar shugaban kasa a zaben na Nijar, yayin da za a zabi 'yan Majalisun dokoki 113.

Zaben ne ake fatan zai kawo karshen ikon gwamnatin rikon kwarya wadda majalisar mulkin sojan CSRD ke jagoranta tun bayan kifar da gwamnatin Malam Mamadou Tandja.