Magoya baya da masu kin Shugaba Mubarak sun kabsa

Masu zanga-zanga a Masar Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana zargin jami'an tsaro na farin kaya da kokarin tarwatsa zanga-zanga

An yi mummunan artabu a tsakiyar Alkahira yayin da masu goyon bayan Shugaba Hosni Mubarak na Masar suka kutsa dandalin Tahrir a kan rakuma da dawaki don kokarin tarwatsa masu zanga-zanga.

Dubban masu zanga zangar kin jinin gwamnati suke ta neman Shugaban ya sauka daga kan karagar mulki ba tare da wata wata ba.

Bangarorin biyu sun yi ta dauki - ba -dadi suna jifar juna da duwatsu da kuma kafsa fada da sanduna da karafan rodi.

Yayin da duhu ya yi, hotunan TV sun nuna gungun ‘yan masar din na jefa buraguzai da bam din fetur daga saman rufin gine gine a kan masu zanga zangar dake kasa.

Jami'ai sun ce an kashe mutum daya, sannan daruruwan mutane sun samu raunuka.

Yayin da ake cikin wannan zaman dar-dar a kasar ta Masar, gwamnatin Nijeriya ta tura jirgin sama domin kwaso 'yan Nijeriya dake filin jirgin saman birnin alqahira din.