A Masar an ci gaba da gwagwarmayar adawa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A titunan Alkahira babban birnin kasar Misra, rahotanni sun bayyana cewa a daren jiya an jiyo karar harbe harbe sannan kuma tayoyi na ci gaba da ci da wuta.

Wannan na faruwa ne kwana daya bayan arangamar da ake yi tsakanin magoya bayan shugaban kasar Husni Mubarak da masu adawa da shi.

Wadanda suka shaida lamarin da idanunsu daga dandalin Tahrir Square sun ce a kalla mutum guda ya rasu sannan da dama sun jikkata, a yayinda masu zanga zanga ke ta tururuwar gujewa tashin hankalin.

An dai yi ta musayar bama baman da aka hada da man fetur da kuma jifan juna da duwatsu.

Dama dai tun ma kafin tashin hankalin ya barke, mutane na cike da fargaba.

Sojoji sun yi ta gargadin mutane da su koma gida, domin samar da zaman lafiya da daidaito a kasar, musamman da ya ke basu da yanda zasu yi su iya shiga tsakani ballantana su dakatar da tashin hankalin.

Al'amuran dake faruwa dai sun sauya akalar abubuwa, wanda hakan ke nuni da cewa 'Yan Masar sun fara kokarin yin juyin juya hali na lumana.