Fulani sun yi kiran neman zaman lafiya a Filato

Masu janaza a jihar Filato Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana ta neman hanyoyin kawo zaman lafiya

Majalisar sarakunan Fulani a Naijeriya ta ce zaman lafiya a jihar Plateau mai samuwa ne in har dai masu fada a ji a jihar sun amince da zaman sasantawa.

Majalisar Fulanin ta kuma wanke 'ya'yanta daga hare-hare na baya-baya da aka sha kaiwa .Ta bayyana hakan bayan wani taron da ta yi da shugabannin Filanin Naijeriya a kan rikicin Jos.

Sun ce sun rubuta wasika ga gwamnan jihar ta Plateau suna neman a zauna a sasanta, amma yau wata kamar ukku ba su sami amsa ba.

Jihar ta Plateau ta yi fama da rikici da ya hada da halaka dimbin rayuka da kona dimbin dukiyoyi.