Mahaukaciyar iska ta ragargaza tekun Queensland

Mahaukaciyar iska ta ragargaza tekun Queensland Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An yi gargadin iskar ka iya yin illa ga yankunan sosai

Iska mai karfi ta soma ragargazar gabar tekun Jihar Queensland ta Australia a inda ake sa ran saukar wata mummunar mahaukaciyar guguwa da ruwa nan gaba kadan.

Wani Magajin garin ya ce tuni ya ga rufin gini ya kwaye, inda mutane 500 ke neman mafaka.

An lalata wata cibiyar binciken yanayi dake cikin teku dake kan hanyar mahaukaciyar guguwar Yasi, sannan layukan wutar lantarki da itatuwa sun fadi.

Magajin garin na Townsville, dake fuskantar mahaukaciyar guguwar, Les Tyrell, ya bayyana cewar wannan mahaukaciyar guguwa na da hadarin gaske:

"Abinda ya kamata mu sani shi ne cewar inda wannan mahaukaciyar guguwa ta dosa zai kai nisan kilomita 400, kuma mai girma ce matuka, mummuna ce ainun".

An kwashe kimanin mutane dubu 30 a birnin Cairns daga gidajensu.

Jami'an Australia sunce mahaukaciyar guguwar za ta iya kadawa har cikin kasa da nisan daruruwan kilomitoci, abinda zai shafi yankunan Queensland da har yanzu suke fadi tashin murmurewa daga ambaliyar ruwan watan da ya wuce.